By Ishaq Dabai
Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ya samar da na’ura mai amfani da hasken rana mai karfi megawat 8 dan bunkasa wutar lantarkin kauyuka da nufin cigaban su.
Kimani gidaje dubu 12,000 daga wurare daban daban a kananan hukumomi Tara (9), dake karkashin masarautar ne zasu amfana da wannan shiri na samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana.
Bangarori uku ne dai suka hadu domin gudanar da wannan aikin, inda suka haɗar da Kamfanin Sandastream Nigeria Limited hadin gwiwa da gwamnatin tarayya da hukumar da take kulada samarwa da kauyuka wutar lantarki (REA).
Da yake magana a yayin bikin kaddamar da shirin shugaban kamfanin na Sandstream Nigeria limited, Alhaji Ibrahim Abba Gana yace kamfanin yana bada tabbacin yin aikin cikin nasara, wanda kuma zai taimakawa manoma da ‘yan kasuwa dake kasuwar Dawanau.
Anasa jawabin sarkin Bichi ya nuna jin dadinsa ga kamfanin da abokan tarayya wajen gabatar da wannan aiki na samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana.
Sarkin na Bichi ya bukaci kwamitin daya hada da hakimai dasu zabi kauyukan da zasu amfana da wannan shiri, sannan ya bukaci ‘yan kasuwar Dawanau da su bada hadin kai wajen gani anyi aikin cikin nasara.