Wata amarya ta janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan bayyanar bidiyon ta wanda ya nuna irin kwalliyar da aka yi mata.
Mutane sun yi ta magana akan irin kwalliyar da aka yiwa amaryar saboda yadda aka cikata kuma ko kaɗan ba tayi kyau ba. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: An cafke wani yaro mai ƙananan shekaru bisa ɗirkawa ƴanmata 10 ciki
Sai dai ita amaryar ko a jikinta, domin samun ganin ta auri wanda take so ya fiye mata duk wani gutsiri tsoma da mutane za suyi ba, domin hakan bai sanya taji takaicin kwalliyar da aka yi mata ba.
A bidiyon wanda @aj_qualitysound ya sanya a Instagram, ya nuna ma’auratan biyu suna ta tiƙar rawa abin su a cikin farfajiyar wajen taron cike da da annashuwa.
A cikin bidiyon wanda tuni har ya karaɗe shafukan sada zumunta, amaryar na sanye da rigar amare fara sannan an yi mata wani gyaran gashi na musamman.
Sai dai abinda yafi ɗaukar hankali dangane da amaryar shine yanayin kwalliyarta wanda yayi kama da kamar ƴar koyo tayi mata.
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su akan bidiyon inda suka yabawa amaryar kan yadda bata bari abun ya dameta ba har ya kai ta ga rashin nuna farin cikin ta.
Ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
tshego9544 ya rubuta:
“Ita ko a jikinta murnar ta kawai take yi, ko ba komai ba ta bari hakan ya ɓata mata muhimmiyar rana a gare ta ba.”
bayathandwa_shembe_ ta rubuta:
“Sun nuna suna cikin farin ciki kuma suɓa tare da juna, shine abinda yafi komai muhimmanci, kwalliyar za tayi kyau a ranar murnar cikar su shekara ɗaya da aure.”
bgg_5445 ta rubuta:
“Wace kwalliya? Mutum biyu kawai na gani cikin farin ciki.”
be11amakula ta rubuta:
“Ina tunanin mijin shine wanda yayi mata kwalliyar.”
mamaga_jenny ta rubuta:
“Aƙalla dai tana cikin farin ciki. Waɗanda ma suke kashe kuɗi a wajen auren su ba su kai ta farin ciki ba.”
Bidiyon namiji mai mazaunai tamkar mace yayin da yake tseren gudu ya ɗauki hankula
Wani bidiyo wanda aka ga wani namiji yana gudu yayin da yake da siffa irin ta mata ya yi matukar daukar hankalin ‘yan soshiyal midiya.
A bidiyon wanda shafin House of highlight na Instagram ya wallafa, an ga yadda da yake sanye da kaya farare.