Kamar yadda tsare-tsare na bukukuwan auren da za’a yi na zawarawa a jahar Kano ana cigaba da awon lafiyar masu sha’awar auren domin tantance lafiyarsu.
Kakakin Hukumar Hisbah, Lawan Fagge, ya ce an dauki wannan mataki na awon lafiya ne a matsayin wani bangare na ka’idojin daurin auren da jihar ta dauki nauyin yi.
An dan samu wasu daga cikin wadanda aka auna da wasu yan matsaloli na rashin lafiya inji Fagge,kuma ya ce tun daga lokacin ne aka maye gurbin mutanen a wannan atisayen da ake yi amma sai aka ba su shawarwari tare da ba su magunguna.
Karanta nanBakada Zabin da Ya Wuce Ka Jira Zabe Na Gaba-APC Ta Fadawa Atiku
A cewarsa wannan ya samo asali ne daga rahoton wucin gadi da muka samu daga ma’aikatar lafiya.
Akwai kimanin maza da mata 40 da ke dauke da cutar Hepatitis B. Akwai masu ciwon sikila, sannan akwai masu ciki da masu dauke da cutar kanjamau. Amma za a yi musu nasiha da ba su magunguna na watanni masu zuwa.
An bukace su da su dage da motsa jiki kuma akwai wanda zai maye gurbinsu. Ana iya la’akari da su idan sun jimre da shawarwari da magunguna.
Mun auna lafiyar kusan 5,000 wanda daga cikin ma’aurata 1,800 kawai muke bukata in ji Fagge.
A wani labarin kumaHadin Kan Yan Najeriya Tinubu Ya Saka A Gaba-Matawalle
Ku tuna cewa jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware Naira miliyan 854 domin gudanar da daurin aure ga ma’aurata sama da 1,800 a jihar.
Ku tuna cewa gwamnatin da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya jagoranta ne ta fara gabatar da daurin auren zawarawa a jihar ta Kano.