An shiga rudani biyo bayan samun rahoton mutuwar daya daga cikin jiga-jigan ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar Labour Party, LP, Humphery Anumudu, a jihar Imo, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
An tattaro a Owerri cewa ranar Asabar, lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata a gidansa da ke jihar Legas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kano Taci Tarar Wadanda Suka Karya Dokar Tsaftar Muhalli
Har zuwa lokacin hada wannan labarin, ba a fitar da wata sanarwa a hukumance daga ‘yan uwa a kai ba. Haka kuma, har yanzu shugabannin jam’iyyar Labour a jihar ba su yi wa manema labarai karin haske kan faruwar lamarin ba.
Sai dai wata majiya ta kusa da jam’iyyar Labour a Imo, wadda ba ta so a ambaci sunanta ba ta ce: “Yan uwana mun rude da abin da ya faru. Hakan ya faru ne a jihar Legas, ka san irin wannan labari ka samu daga dangi ko kuma shugabancin jam’iyyar LP.
“Ya halarci taron kwamitin ayyuka na kasa, masu neman kujerar gwamna, da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Abuja a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris, 2023.
Dole ne ya garzaya zuwa Legas washegari, Juma’a, don tattara muhimman takardu da ake buƙata don zaɓen fidda gwani na gwamna da za’a gabatar a ranar 15 ga watan Afrilu, 2023.”
Anumudu na daga cikin mutane goma sha uku masu neman kujerar gwamna a jam’iyyar Labour, wadanda suka sayi fom dinsu har naira miliyan 25. Idan dai za a iya tunawa, Anumudu ya kasance a wannan takara ta neman kujerar gwamnan Imo tun daga jam’iyyar, PDP. Shahararren dan kasuwa ne mai nasara.
A wani labarin kuma, Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mashawarcin Gwamnan Zamfara
Wasu ‘yan bindiga sun sace mai bayar da shawara na musamman ga gwamna Bello Matawalle kan harkokin siyasa a jihar Zamfara.
An sace Hon Ibrahim Maaji ne a gidansa da ke unguwar Mareri a cikin garin Gusau, babban birnin jihar da sanyin safiyar Asabar din nan.