Kotun tafi da gidan ka da gwamnatin Kano ta samar, domin hukunta waɗanda suka bujirewa dokar tsaftar muhalli ta karshen wata, ta Kama mutane 34 da lefin karya dokar.
A Asabar din nan ne aka gudanar da Tsaftar Muhallin wadda ta kasance doka, da kuma take farawa daga 7am zuwa 10 na safe.
KU KARANTA: Tambuwal Yayi Rashin Kwamishina
Kotun karkashin jagorancin Majistire Auwal Yusuf Suleiman ta Sami mutanen 34 da lefin karya dokar inda aka yi musu tarar naira dubu 40.
Da yake ganawa da manema labarai Jin kadan bayan duba yadda aikin tsaftar Muhallin ya gudana a Kano, kwamishinan ma’aikatar Muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ja kunnen matuka baburan adaidaita sahu wanda su aka fi kamawa da lefin, akan su guji karya dokar.
Domin kuwa a cewarsa Gwamnatin Jihar Kano ba za ta zuba Ido a cigaba da aikata laifuka Ba.
Ya ce Gwamnati a shirye take wajen daukar dukkan matakan da suka da ce domin rage ko kawo karshen aikata laifukan da suka danganci tsaftar Muhalli a fadin jihar.
Kwamishinan ya yabawa al’ummar jihar Kano bisa yadda suke bin dokar ta zaman gida tare da tsaftace yankunan su.
A wani labarin kuma: Bankuna Suna Bi Umarnin Bankin CBN Na Yin Aiki A Ranekun Karshe Makonni
A ranar Asabar ne aka bude bankunan kasuwanci a birnin tarayya Abuja domin gudanar da kasuwanci kamar yadda babban bankin Najeriya CBN ya umarta.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, wanda ya sa ido a kan wasu bankunan yankin, ya ruwaito cewa an ga dimbin kwastomomi a rumfunan bankunan da ke injin cirar kudi (ATM).