By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar dokokin jihar Ebonyi ta zabi tare da rantsar da sabon mataimakin kakakin majalisar Hon Kingsley Ikoro mai wakiltar Afikpo ta Arewa Maso Yamma.
Amma mataimakin kakakin majalisar da aka kora, Hon Obasi Odefe, mai wakiltar Onicha ta Gabas, ya bayyana matakin a matsayin shirme da hauka.
Zaben Ikoro ya biyo bayan kudirin da Honarabul Onu Nwonye mai wakiltar Ohaozara ta Yamma ya gabatar kuma Hon Anthony Nwegede na Izzi ta Gabas ya goyi bayansa tare da wakilai 15 cikin 24 da suka halarci zaman majalissar.
Kudirin ya zo ne sa’o’i 24 bayan da Honarabul Odefe ya koka kan shirin tsige shi a ranar Asabar.
Idan dai zaku iya tunawa a ranar 21 ga watan Fabrairun 2022 Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shugaban majalisar, Rt.Hon. Francis Nwifuru, ya bayyana cewa su biyun sun yi murabus daga zama ‘yan majalisar dokokin jihar.
Sai dai Odefe, wanda ya zanta da ‘yan jarida ‘yan mintoci bayan zaman majalisar, ya ce bai yi murabus daga mukaminsa na mataimakin kakakin majalisar ba kuma bai koma jam’iyyar APC ba.
Ya ce, “Abin da ya faru a gidan yau hauka ne don mulki, Don haka, ni ne mataimakin shugaban majalisar.”