Rikicin shugabancin masallacin Darul Hadith na marigayi Dr Ahmad Ibrahim BUK na unguwar Tudun Yola ta jihar Kano, ya kawo tsaiko wurin gudanar da sallar Juma’a a ranar Juma’a.
Rigima ta fara ne lokacin da wasu fusatattun mutane suka tare hanyar sabon limamin masallacin wanda yake ƙoƙarin hawa mumbari domin yin huɗuba sannan ya jagoranci Sallah. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
KU KARANTA: Yadda magidanci ya bindige matarsa har lahira bisa rashin sani
Limamin ya cije lallai sai ya jagoranci Sallah inda yayi ƙoƙarin wucewa amma mutanen suka riƙe masa alkyabbar sa.
A na cikin hakan ne sai jami’an suka shiga cikin lamarin sannan suka kewaye masallacin yayin da wasu masallata suka kama ficewa.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga majiyar mu, kakakin hukumar ƴan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, yace ƴan sanda ba su yi wata-wata ba yayin da suka samu rahoton lamarin.
“Kwamishinan ƴan sanda ya bayar da umurnin tura jami’an mu domin kare sake tashin wata hatsaniyar.
Jami’an mu sun samu nasarar shawo kan lamarin sannan an gudanar da Sallar ba tare da wata matsala ba. A halin da ake ciki kuma an gayyaci ɓangarorin biyu domin amsa tambayoyi. A cewar sa.
Mazauna Tudun Yola inda masallacin yake, sun cigaba da gudanar harkokin bayan aukuwar lamarin.
Yadda Ƙaramin Yaro Ya Kitsa Sace Mahaifinsa, Ya Karɓi Maƙudan Kuɗaɗen Fansa
A wani labarin na daban kuma, wani yaro ya shirya yadda za a sace mahaifin sa sannan ya karɓi maƙudan kuɗaɗen fansa.
Hukumar ƴan sandan jihar Kwara ta samu nasarar cafke wani mai suna Issa Naigheti bisa zargin yin garkuwa da mahaifin sa da amsar kuɗin fansa Naira miliyan biyu da dubu ɗari biyar (N2.5m).
Kakakin hukumar ƴan sandan, Ajayi Okasanmi, wanda ya bayyana hakan yace an cafke wanda ake zargin ne a kusa da yankin Kambi na Ilorin.