Wasu al’umma a shafin sada zumunta sun hada hannu wajen tallafawa Malam Yakubu da jarin domin sana’a. Wannan ya biyo bayan tunani da wani mutum mai suna Abdullahi O Haruna Haruspice ya yi bayan da ya rubuta wata maka akan Malam Yakubu wanda yake shima tsohon dalibin Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ne, inda ya karanta bangaren sanin halayyar Dan Adam, amma kuma ya koma sana’ar sayar da katin waya a gaban ginin dakunan kwanan dalibai na Suleiman Hall dake Jami’ar.
Duk da Malam Yakubu ba kudade masu yawa yake samu ba sama da shekara 20 da yake sayar da katin wayar, amma yana da taimakon dalibai a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Majiyarmu ta Abusites ta labarto cewa; mutane dama ne ba tare da nuna bambamcin addini ko kabila ba suka tattaru waje guda suka tallafawa Malam Yakubu.
Ga jerin mutanen da suka tallafa masa;
Sama’ila Ahmad;. ₦1000
Yusuf Abdulmmin;. ₦2000
Abdulhakim Ibrahim;. ₦1000
Adejo Sam Okedi;. ₦50, 000
Adamu Alhasan Umar;. ₦10, 000
Kamaludeen Ahmad Kamaludeen;. ₦2000
Sanni Islamiat Okikiola;. ₦20, 000
Eragbe Anslem;. ₦5000
Helpline Foundation/Ahmadu Jumai;
₦20, 000
Isma’il Halisa;. ₦1000
Amira Omobolanle Khalid;. ₦2000
Livonda Alphonsis James;. ₦500
Nasiru Ola Shehu;. ₦1000
Vincent Unogwu;. ₦2000
Dalhatu Abubakar;. ₦40, 000
Anonymous;. ₦10, 000
Usman Liman;. ₦1000
Gondyi Nengak Daniel;. ₦5000
Mariam Negedu;. ₦2000
Bilyaminu Gobirawa Bello;. ₦1000
Tijani Saheed Oladele;. ₦2000
Haidare Aminu Ibrahim;. ₦2000
Abdul Rahman Ibrahim Gagari; ₦3000
Ahmadu Muhammad;. ₦1000
Abioye Afeez Ayuba:. ₦2000
Isah Mohammed Aliyu;. ₦1000
Chimewave Inc;. ₦5000
Jamilu Ibrahim Dauda;. ₦100
Abdullahi Haruna O. Haruspice ₦3000
Adadin kudin da aka tattara:
₦199, 600.00
An tara naira dubu dari da casa’in da tara da dari shida, inda bayan tara kudin an ziyarci Malam Yakubu inda aka tambaye shi wata sana’ar zai rika yi bayan sayar da katin wayarsa. Inda ya tabbatar da cewa idan da a ce yana da jari, zai fara sayar da kayayyakin waya ne wanda ya ce akwai riba a sana’ar.
Inda nan take aka shawarci Malam Yakubu da matarsa akan su yi amfani da kudin wajen yin sana’a. Nan take aka ba Malam Yakubu Naira dubu 100 domin yin sana’ar sayar da kayayyakin waya da bunkasa sana’arsa da katin waya.
Ita kuma matarsa aka bata naira dubu hamsin domin ta rika sana’o’in gida. Sannan aka saya shinkafa mai nauyin kilogiram 50, da katan na Taliya, da katan na Macaroni da man gyada da manja da buhun masara da sabulun wanka da na wanki inda aka ba su domin tallafawa gidansu.