Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tattalin Arzikin Kasar na habakar da ba a taba ganin irinta ba a bana, tun bayan karbar mulkinsa. Inda ya ce, a yanzu tattalin Arzikin ya samu tagomashin karin kaso 5.01% a tsakiyar wannan shekara.
To sai dai ikirarin shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da talakawan kasar ke dandana kudarsu ta fannin hauhawar farashin kayan masarufi, musamman ma kayan abinci wadanda farashinsu ya yi tashin gwauran zabi a kasuwannin Kasar.
‘Yan Nijeriya da dama da majiyarmu ta zanta da su sun bayyana cewa su dai ba su ga habakar tattalin arzikin ba, domin a kowacce rana kayayyakin masarufi musamman kayan abinci kara tsada suke.