Babbar Kotun Majistare dake Makurɗi a ranar Juma’a ta bada umarnin tsare mutane huɗu a gidan gyaran aƙida sakamakon zargin su da kone gonar Mangwaro na gonar tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo.
Waɗanda ake zargin sun ƙunshi: Julius Igyo, da Samuel Aleva, da Pius Mcha, da Kuma Daniel Oryserga dukkanin su, sun fito daga Ƙaramar Hukumar Gwer ta Gabas dake Jahar Benue.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Adamawa Za Ta Hana Sayar Da Dabbobi, Da Safarar Su Zuwa Legas, Da Sauransu Jihohi
Ana tuhumar su ne akan aikata ta’addanci, da hassala husuma, da tsallake gona da iri, sanya wuta da gayya.
Babban Majistare Vincent Kor bai yarda da wani uzuri daga waɗanda ake zargin ba, sai ya ɗage shari’ar zuwa 28 ga watan Maris domin cigaba da shari’ar.
Tunda Farko mai shigar da Ƙarar Sajan Godwin Ato, ya shaidawa Kotu cewa a ranar 31 ga watan Janairu, Manajan Gonar Suberu Mohammed ya kawo rahoton faruwar lamarin ga Kwamishinan Ƴan Sandan Jahar Benue.
Mr Ato yace Manajan yace a ranar 29 ga watan Janairu, ya samu wayar tarho daga mataimakin sa Gowon Tarkev wuta ta kama a gonar.
Ya bayyana cewar a lokacin da yayi saurin zuwa gonar, ya gano cewa wutar ta ƙone tsawon safiya 90 na gonar, daya ƙunshi mangwaro dubu 18,360 da kuɗin su yakai Naira Miliyan 183.6.
Manajan a cikin sanarwar ya ƙalubalanci waɗanda ake zargin da haddasa faruwar wannan lamari.
Yace waɗanda ake zargin da farko sun buƙaci a biyasu diyya akan gonar su da aka shuka Mangwaro, kuma suna yawan dukan su, da yiwa rayuwar su barazana, gami da sare itatuwan Mangwaro.