An tsige shugaban wata Ƙaramar Hukuma a Najeriya akan Zargin karkatar da Kuɗi
Kansilolin karamar hukumar Ijebu ta gabas a Jihar Ogun a ranar Alhamis sun tsige Shugaban ƙaramar hukumar da aka dakatar Hon Wale Adedayo bisa zargin karkatar da kuɗaɗen ƙaramar hukumar.
Shugaban Majalisar Kansilolin Honorabul Fasheyi Akindele a wata sanarwa da ya fitar ya ce an tsige Adedayo ne bayan ya bayyana a gabansu biyo bayan gayyatar da aka yi masa kan zargin karkatar da kudaden.
A cewar Akindele bayan gayyata a lokuta daban-daban da suka yi ma dakataccen Shugaba daga bisani Adedayo ya bayyana a gabansu yayin da kansilolin suka ci gaba da Bincike akan shugaban ƙaramar hukumar.
Kansiloli 11 ne suka halarci zaman inda aka tsige Adedayo.
KARANTA NAN:Kwastam sun kama Fatar Jakuna da Man fetur na sama da Miliyan 19 da akayi fasa Ƙwabrin su
An kuma ce Shugaban da aka dakatar ya kashe kuɗaɗen ƙaramar hukumar har zuwa watan Agustan shekarar 2023 duk da cewa ba a amince da kasafin kudin ba, maimakon yadda doka ta ba shi damar kashewa zuwa watan Maris na shekarar 2023 kawai.
Haka Zalika Shugaban Majalisar Kansilolin ya bayyana cewa, Shugaban ƙaramar hukumar da aka dakatar ya karya dokoki daban-daban, musamman dokar karamar hukumar Jihar Ogun ta shekarar 2006, tare kuma da aikata manyan laifukan da za su iya sanyawa a tsige shi.
Bayan da aka gudanar da zaman, an kada kuri’a kan tsige Shugaban, inda Kansiloli 5 suka kaɗa kuri’ar tsige shi, hudu kuma suka kaɗa kuri’ar kin amincewa, yayin da kansila 1 bai yanke hukunci ba.
Daga nan ne Shugaban Majalisar Kansilolin ya bayyana cewa an tsige Mista Wale Adedayo a matsayin Shugaban karamar hukumar Ijebu ta gabas,” in ji Akindele.
Da yake mayar da martani dangane da hukuncin, Shugaban ƙaramar hukumar Mr. Adedayo ya ce duk abinda ya fara shiryayye ne, ya kara da cewa bai aikata wani laifi ba.
Ya ce, “Na gaya musu cewa suna amfani ne da ƙagaggun tuhume-tuhume, amma na san Gwamna ya ji haushin yadda muka bayyana wa jama’a dangane da yadda rabon kuɗin tallafin Gwamantin tarayya ya kasance.
“Na yi aikina a matsayina na Shugaba ta hanyar sanar da shugabanmu dalilin da ya sa muka kasa yin wani abu da yawa tun da muka hau ofis, saura kuma kotu ce za ta yanke hukunci”, inji shi.