Daga: Penina Jeje Ali Damaturu
Shugaban jam’iyyar APC ta jihar Yobe, Alh. Mohammed Gadaka yayi ta’aziya ga iyalan marigayi Abdul Wasi’u a ranar Laraba a gidan ss da ke karamar hukumar Potiskum ta jihar Yobe.
A cikin wata sana’arwa mai dauke da rattaba hannun sakataren hulda da yan jaridu na shugaban jam’iyyar APC, Sa’adatu Maina, Gadaka ya bayyana cewar mutuwar Abdul Wasi’u a matsayin babbar rashi ga iyalan shi, da al’ummar Potiskum dama wakilan jam’iyyar APC a fadin jihar.
KARANTA WANNAN: Tinubu Ya Umurci Shugaban FIRS ya Tafi Hutun Ritaya Kafin Ya Yi Ritaya
“Marigayi Abdul Wasi’u abokin tafiya ne mai kirki wanda ya bada gudunmawa sosai wajen samun cigaban jam’iyyar APC a jihar, in Sha Allahu zamu jima tare da tunawa da ire-iren gudunmawa da yabawa jihar Yobe” inji Alh. Gadaka.
Ya bayyana rashin jin dadin sa, sanan yayi addu’ar Allah ya karbi bakoncin Abdul Wasi’u, sanan ya karawa iyalan sa hakurin jure rashin.
Alh. Mohammed Gadaka ya kuma yi addu’ar Allah yasa Aljannatul firdaus ce makomar ayyukan alkhairi dayayi.
A wani labarin kuma,Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Yi Sabon Nadi a Gwamnatinsa Bayanai Sun Fito
Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Zaccheus Adedeji a matsayin sabon shugaban riko na hukumar tara haraji ta tarayya (FIRS).
Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Ajuri Ngelale ya fitar, ta ce shugaban ya kuma umarci tsohon shugaban FIRS, Mista Muhammad Nami, da ya ci gaba da hutun watanni uku na hutun ritaya, kamar yadda dokar ma’aikatan gwamnati (PSR) ta tanada 120243, tare da sakamako nan take.
Fadar shugaban kasar ta bayyana cewa hutun kafin ya yi ritaya zai kare ne daga karshe ya yi ritaya daga aiki a ranar 8 ga watan Disamba, 2023.
“Hon. Zacch Adedeji an nada shi ne a matsayin mai rikon kwarya na tsawon kwanaki 90 kafin a tabbatar da shi a matsayin babban Shugaban Hukumar tara Harajin Cikin Gida ta Tarayya na tsawon shekaru hudu (4) a matakin farko.