An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Da Ta Ɓata A Abuja
An tsinci gawar wata dalibar Jami’ar Najeriya, NOUN, Blessing Karami, wadda aka bayyana batan ta ranar 11 ga watan Satumba a babban birnin tarayya, Abuja.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh ya tabbatar wa DAILY POST hakan a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Ɗumi-Ɗuminsa: Kotun daukaka kara ta tabbatar da Mbah a matsayin Gwamnan Enugu
Ta ce an gano gawar ta ne a wani daji da ke yankin Karimo na babban birnin kasar.
A cewar ‘yan sanda, an kai rahoton bacewar dalibar mai shekaru 26 ga hukuma a ranar 14 ga Satumba, 2023.
PPRO ta ce kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, CP Haruna G. Garba ya bayar da umarnin gudanar da kwakkwaran bincike kan “al’amuran da suka dabaibaye Blessing Karami Moses har ya kai ga mutuwar ta.
Ta kuma bayyana cewa, jajircewar da hukumar ta yi kan lamarin kisan gilla ne, kuma ta kuduri aniyar gano musabbabin faruwar lamarin nan take.
Ta ce a halin yanzu rundunar tana aiki tare da hukumar kare muhalli ta Abuja, AEPB domin kwato gawar da ta lalace.
“Za mu ci gaba da samar da bayanai ga jama’a yayin da bincikenmu ke ci gaba da tafiya.
“Tunanin mu yana tare da iyalai da masoyan Blessing Karami Moses a wannan mawuyacin lokaci”, in ji PPRO.
A wani labarin kuma:Zan Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara – Dan takarar PRP
Dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a jihar Enugu, Chris Agu, ya sha alwashin daukaka kara kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar ta yanke kan zargin yin bogi na NYSC da Gwamna Peter Mbah ya yi.
Agu ya yi wannan alwashi ne a Enugu ranar Alhamis yayin da yake mayar da martani kan korar da kotun ta yi na kalubalantar takardar shedar aikin yi wa kasa hidima (NYSC) da Gwamna Mbah na jihar Enugu ya yi.