Hukumar dakile cututtuka ta Nijeriya wato NCDC ta tabbatar da cewa ya zuwa daren jiya Litinin ana da tabbacin mutum 665 sun kamu da cutar Korona daga jihohin kasarnan, bayan da aka samu karin mutum 38 a jiya kawai. Ta tabbatar da hakan ne a shafinta na Twitter.
Inda kuma mutum 22 suka mutu daga cutar a yayin da 188 suka warke daga cutar. A jiya Litinin an gano mutum 38 masu dauke da cutar daga jihohi 8. Wanda suka hada da;
23 a Kano
5 a Gombe
3 a Kaduna
2 a Borno
2 a Abia
1 a FCT
1 a Sokoto
1 a Ekiti
Jihar Kano na adadin mutum 59 masu dauke da cutar ya zuwa yanzu.