Taron tsofaffin shugabannin mata na jam’iyyar APC na shiyyar Arewa ya yaba wa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin bisa yadda ya dauki mata a ayyuka daban-daban.
Mambobin dandalin na shiyyoyin siyasa shida na kasar nan sun kai ziyarar ban girma ga mataimakin shugaban majalisar dattawa a harabar majalisar dattawan Abuja. Shugabannin matan sun samu jagorancin tsohuwar shugabar matan shiyyar Arewa maso Yamma a jam’iyyar APC, Hajiya Yahanasu Buba Ahmed.
KARANTA NANDage Takunkumin Zuwa Dubai,Tinubu Yayi Abin A Yaba Mashi-Akpabio
Da take jawabi yayin ziyarar, wata tsohuwar shugabar mata ta shiyyar Kudu-maso-Kudu ta jam’iyya mai mulki, Misis Racheal Akpabio, ta ce mataimakin shugaban majalisar dattawa bai nuna wariya ga mata a nade naden masu taimaka masa.
Muna sane da dimbin abubuwan ci gaba da kuke yi a jam’iyyarmu. Abu mafi mahimmanci shine kada ku nuna bambanci tsakanin mata da maza a duk abin da kuke yi, kuna ɗaukar mata tare. Muna godiya da wannan.
Wasu daga cikinmu jiga-jigan jam’iyyar ne tun 2014. Mun kai jam’iyyar zuwa lungu da sako na kasar nan. Ba mu gaji ba, ba mu yi ritaya ba, kuma muna jiran a kira mu mu hada karfi da karfe don isar da ribar dimokuradiyya ga ‘yan kasa.
Mu masu kishi ne, masu hankali, kuma masu aminci ne kamar yadda kakakin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ismail Mudashir ya fitar, ya nakalto ta.
Da yake mayar da martani, Barau ya yabawa shugabannin matan kan sadaukarwar da suka yi wa jam’iyyar. Hakan a cewarsa ya taimaka wajen samun nasarar jam’iyyar APC tsawon shekaru.
Ya kuma yabawa shugaban kasa Bola Tinubu da uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi, bisa jajircewar da suka nuna wajen kawo mata a mukamai daban-daban domin ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kasa.
A WANI LABARIN KUMAKu Daga Darajar Aikin Gwamnati Da Kwarewarku-Mai Mala Ga Sabbin Manyan Sakatarori
Sadaukarwar da kuka yi tun da aka kafa babbar jam’iyyarmu, APC tana da yawa tana dawwama, kuma ba za a iya mantawa da ita cikin sauki ba,kunyi sadaukarwa mai yawa ta fuskar lokaci da dukiya don samun nasarar jam’iyyarmu a kowane mataki.
Saboda sadaukarwa, sha’awa, da aminci, za mu tabbatar da cewa an ba ku fifikon da ya dace ta hanyar nade-nade a cikin jam’iyyarmu da kuma cikin gwamnati,” in ji Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan.