Hukumar alhazai ta jihar Kogi ta ce an fara shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin shekarar 2014 da gaske, kuma ana sa ran dukkan maniyyatan masu niyya zasu fara yin ajiya domin gudanar da aikin.
A wata sanarwa da shugaban hukumar Sheikh Luqman Imam Abdullahi ya sanyawa hannu a ranar Laraba ya ce kowane mahajjaci zai yi ajiya mafi karanci Naira (Miliyan hudu da Naira dubu dari biyar, 4,500.000) kacal.
KARANTA WANNAN: Imo 2023: LP ta Kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamna Mai Wakilai 481
Ya kara da cewa hanyar biyan duk wani mahajjaci shine ya bude asusun ajiyar aikin Hajji (HSS) a bankin Jaiz (Lokoja), yana mai cewa lokacin biyan kudi yana tsakanin yanzu da watan Fabrairun shekarar 2024.
Sanarwar ta ce ‘Hukumar alhazai ta jihar Kogi na son sanar da daukacin al’ummar musulmin jihar da kewaye cewa an fara shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji na shekarar 2024 gadan-gadan.
Mahajjata masu zuwa su lura da waɗannan buƙatu masu zuwa: Mafi ƙarancin ajiya: shine Naira (Miliyan Hudu da Naira Dubu Dari Biyar, 4.500.000) da Lokacin Biyan: Tsakanin Yanzu zuwa watan Fabrairu 2024
Sauran buƙatun su ne: Hanyar biyan kuɗi: Buɗe tsarin tanadin aikin Hajji (H.S.S) tare da bankin Jaiz (Lokoja) Samun kujera yana da iyaka.
Mahajjatan masu niyya zasu iya ziyartar ofishin Hukumar da ke Lokoja domin jin karin bayani, ya kara da cewa lokaci ya na da matukar muhimmanci saboda mahukuntan Saudiyya na da tsauraran lokaci.
A wani labarin kuma, Ambaliya: Gwamnatin Benue Za Ta Bude Hanyoyin Ruwa Da Suka Toshe
Gwamnatin jihar Benue ta ce za ta bude hanyoyin ruwa da suka toshe domin kaucewa afkuwar ambaliyar ruwa a jihar.
Kwamishiniyar hadin gwiwa, raya birane da karkara, Hon. Joy Luga, ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ke rangadin yankunan da ake fama da ambaliyar ruwa domin sanin irin barnar da ruwan saman da aka yi a jihar ya haddasa.