By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin Myanmar ta daure hambararriyar shugabar kasar Aung San Suu Kyi a ranar Litinin na tsawon shekaru hudu saboda tsokanar sojoji da keta ka’idojin Covid 19 in ji wani mai magana da yawun gwamnati wanda ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP, inda yace wannan shine farkon jerin hukuncin da za a iya ganin wanda ya lashe kyautar Nobel a kurkuku shekaru da yawa.
Suu Kyi, mai shekaru 76, tana tsare tun bayan hambarar da gwamnatinta a ranar 1 ga watan Fabrairu, wanda ya kawo karshen wa’adin mulkin dimokuradiyyar kasar a kudu maso gabashin Asiya.
Tuni dai ake tuhumarta da tuhume-tuhume da dama da suka hada da karya dokar sirri, cin hanci da rashawa da kuma zamba a zabe, kuma za ta fuskanci zaman gidan yari na shekaru da dama idan har aka same ta da dukkan laifukan.
A ranar Litinin ne aka yanke wa Suu Kyi hukuncin daurin shekaru biyu saboda tada hankali ga sojoji da kuma wasu shekaru biyu saboda keta dokar cutar Covid 19, kakakin gwamnatin mulkin soja Zaw Min Tun shine wanda ya shaida wa manema labarai.
An kuma daure tsohon shugaban kasar Win Myint na tsawon shekaru hudu bisa wannan tuhume-tuhumen, amma ya kara da cewa har yanzu ba za a kai su gidan yari ba.
“Za su fuskanci wasu tuhume-tuhume daga wuraren da suke zama a yanzu,” in ji shi, yayin da yake magana kan tsare su a babban birnin Naypyidaw amma ba tare da yin karin bayani ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an dai hana ‘yan jarida shiga wata kotu ta musamman dake Naypyidaw kuma a kwanan baya an dakatar da lauyoyin Suu Kyi daga yin magana da manema labarai.
A cikin ‘yan makonnin nan, an kammala shari’ar wasu manyan jami’an kungiyar ta Suu Kyi ta National League for Democracy, tare da yanke hukumci masu tsanani akan su.
Kazalika an yanke wa wani tsohon babban minista hukuncin daurin shekaru 75 a gidan yari a wannan watan, yayin da aka daure wata mataimakiyar Suu Kyi shekaru 20.
Sai dai kuma bayan yanke hukuncin kungiyar Amnesty ta yi Allah wadai da hukuncin da aka yanke wa Suu Kyi.