An sace wani jami’in zabe a jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin Najeriya a ranar Juma’a, sa’o’i kadan kafin zaben gwamnan jihar da za a yi ranar Asabar a jihar mai arzikin man fetur.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), wacce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar da misalin karfe 10 na dare. a ranar Juma’a, in ji jami’in da aka sace jami’in sa ido, wanda aka sanya wa yankin rajista mai lamba 06, Ossioma, a karamar hukumar Sagbama ta jihar – yana jiran ya hau jirgin ruwa a Amassoma Jetty zuwa yankin da aka tura shi aiki.
Karanta nanGwamnan Jahar Nasarawa Ya Yi Zama Da Shugabannin Fulani Akan Matsalar Tsaro
Shugaban sashen wayar da kan masu kada kuri’a a jihar Bayelsa, Wilfred Ifogah ne ya fitar da sanarwar.
Sanarwar ba ta bayyana sunan jami’in da aka sace ba amma dai ta tabbatar da garkuwar kuma ta bayyana cewar jam’inta ne.
Mista Ifogah ya kuma bayyana a cikin sanarwar cewa wani jirgin ruwa dauke da wasu jami’an zabe zuwa Koluama da ke karamar hukumar Sagbama ta jihar ya kife a ranar Juma’a.
Ya ce an kubutar da dukkan jami’ai 12 da ma’aikacin kwale-kwalen ba tare da wani rauni ba, amma sun yi asarar takardar sakamakon zaben da jakunkuna dauke da kayansu.
A wani labarin kumaNa Yi Da Na Sanin Canza Halitta Ta Zuwa Mace–Dan Daudu Jay Boogie
Jimillar wadanda suka yi rajista a yankunan da abin ya shafa sun kai 5,368, sannan adadin PVC da aka tattara ya kai 5,311. INEC na kokarin ganin an gudanar da zabe a yankin da abin ya shafa.
An sanar da hukumomin tsaro in ji Mista Ifogah kuma sun bayar da tabbacin cewar za su bi kadin abin kuma su zakulo wadanda suka aikata laifin.