Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, zaman jira ya haɗa su da tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Haduwar tasu ta zo bayan da suka hadu da a dakin jiran manyan baki na filin jirgin saman Malam Aminu Kano, dake jihar Kano.
KARANTA ANAN: Yajin Aikin ASUU: Gwamnatin Tarayya Tayi Amai Ta Lashe Kan Umarnin Buɗe Jami’o’i
Cikin hoton daya bayyana a yammacin yau din bayan haduwarsu, an hangi fuskar gwamnan Kano Ganduje cikin fara’a, yayin da ta Sanata Kwankwaso babu yabo ba fallasa.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Sanata Kwankwaso dai shine ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, kuma ba sa shiri irin na siyasa da gwamna Ganduje, wanda tsohon mataimakin ne lokacin da Kwankwason na gwamna.
A wani labarin kuma: Ba Zan Bari Ayi Amfani Da Banbancin Addini Wajen Tarwatsa Zaman Lafiyar Kano Ba – Inji Ganduje
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jaddada aniyar gwamnatin sa ta ganin an kara samun zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai a fadin jihar nan.
Gwaḿnan ya sanar da hakan yayin rantsar da ‘yan kwamitin wakilan addinai wanda ya gudana dakin taro na Africa House dake fadar gwaḿnatin Kano.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Ganduje yace gwamnati ba zata amince wasu tsirarun mutane ciki har da ‘yan siyasa suyi amfani da banbancin addinai wajen haifar da rashin fahimta ba, a tsakanin mazauna jihar.