Shugaban asibitin Barau Dikko dake Kaduna Abdulkadir Tabari ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da malaman makarantun horad da likitoci da su inganta darussa da karin likitoci domin kawar da matsalolin karancin Likitoci da ake fama da shi a yanzu a kasar Nijeriya.
Tabari ya yi shi wannan bayanain ne a wani taron gangami na kungiyar likitocin Nijeriya NARD da aka yi a garin Kaduna ranar Alhamis.
Ya kara bayyana cewar shi al’amarin karancin likitoci da ake fama da shi a kasar Nijeriya, abin ya samo asali ne a dalilin rashin inganta makarantun horad da likitoci wadanda suke a kasarnan a dalilin haka ne kuma yasa dalibai da kuma kwararrun likitoci ke ficewa zuwa kasashen waje.
Tabari ya kara jaddada cewar a sakamakon binciken da WHO ta gudanar ya nuna cewar rashin inganta makarantun horad da likitoci ya sa ake samun kwararrun likitoci akalla 0.37 daga cikin mutane 1000 a kasar nan. Bayannan kuma ita kungiyar likitocin hakora ta Nijeriya (MDCN) ya bayyana cewar likitoci 72,000 suka yi rajista da kungiyar wanda daga ciki 35,000 ne ke aiki a cikin kasar Nijeriya.
“Hakann kuma na nuna cewa likita daya ne ke duba marasa lafiya 5,700 a kasar Nijeriya, nan a maimakon likita daya ya duba marasa lafiya 600 bisa ga tsarin kula da lafiyar iyali ta WHO. “A lissafa Nijeriya na bukatar karin likitoci 290,000 idan har ana so a samu gaggarumar nasara a fannin kiwon lafiya na shi kasar Nijeriya.”
Tabari ya yi kira ga kungiyoyin ma’aikatan kiwon lafiya da su hada hannu da gwamnatocin jihohi domin gina makarantu da asibitocin horad da likitoci. Ya kuma kara yin kira da gwamnatocin Nijeriya da kuma na arayya da kuma na jihohi da su hada karfi da karfe da hamshakan ‘yan kasuwa na Nijeriya domin samar da ingantattun kayayyakin aiki a asibitocin kasar nan.