Rahotannin da suka shigowa Jaridar Dimokuradiyya, ya nuna cewa; an yiwa wani matashin dan kasuwa kisan Gilla a kan sana’ar shi A Rigasa Kaduna.
Bayanai sun nuna cewa; matashin dan kasuwar, katin waya yake sarowa yana bi shago-shago yana siyarwa har Allah ya daga shi, ya bunkasa mishi Arziki.
Wasu wadanda ba a san ko su wanene ba, suka yi Asubanci gidansa a wannan babbar rana ta Juma’a suka hallaka shi!
Arewa Daily Post ta labarto cewa; sun kashe shi sun bar ‘ya’yan shi mata Uku kanana, babbar ciki bata wuce shekara 4 ba!
Mamacin mai suna Muhammad Abdullahi Namadi, wanda aka fi sani da Namadi Mai Katin waya, ya samu ci gaba a rayuwarsa, domin har kamfanin MTN sun bashi matsayin babban dillalin su a Rigasa, kuma ana zargin wasu masu bakin ciki da ci gaban shi ne suka hallaka shi.
Za a yi jana’izarsa a babban Masallacin Juma’a na garin Rigasa.