Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa tace sama da ƴan Najeriya Miliyan 3 sun karɓi rigakafin cutar Covid-19.
Babban Daraktan Hukumar Dr Faisal Shuaib, ya bayyana haka a taron Kwamitin Shugaban Ƙasa na mako biyu akan cutar a ranar Litinin a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labaru ya ruwaito cewar an yiwa sama da ƴan Najeriya Miliyan 3 a cikin watanni uku, bayan da ƙasar ta fara rigakafi ga ƴan Ƙasar ta akan cutar Corona.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyar ADP Ta Goyi Bayan Tsarin Yar’tinke
Shu’aib yace kimanin ƴan Najeriya Miliyan 5,891,305 suka karɓi rigakafi na farko na cutar Covid-19, wanda ya bayyana kashi 5.3 na yawan mutanen ƙasar.
Ya ƙara dacewa, kimanin ƴan Najeriya Miliyan 3,252,067 sun karɓi rigakafin su na biyu kuma an yi masu rigakafin, wanda ya bayyana kashi na 2.9 na yawan mutanen ƙasar.
Ya bayyana cewar yawan mutanen da suka isa a yiwa ƴan Najeriya rigakafin Covid-19 yakai Miliyan 111,776,503.
Shugaban Hukumar yace Gwamnatin Tarayya tana da adadin rigakafin da ake buƙata a jiye da zasu isa a yiwa mutane masu yawa rigakafi.
Ya ƙara dacewa ƙasar ta karɓi rigakafin AstraZeneca kimanin Miliyan 3,924,000 a tsakanin 22 ga watan Oktoba zuwa 25 ga watan.
Comments 1