Shugaban jam’iyyar ADP na kasa Alh. Sani Yabagi, a ranar Litinin ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanya hannu kan dokar zabe, yana mai cewa zai kawo gaskiya a tsarin zaben.
Yabagi ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake gabatar da shirin Siyasa na gidan Talbijin na Daily Trust TV.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai Majalisar Dattawa da ta Wakilai suka zartar da kudurin dokar gyara dokar zabe, inda ta amince da watsa sakamakon zabe ta hanyar Na’ura Mai Kwa-kwalwa da na fitar da Dan takara kai tsaye.
Yabagi ya ce: “Mun samu ci gaba. Tare da fitar da Dan takara kai tsaye, kun ba wa mutane ikon zabar Wanda suke so. ”
Ya bayyana siyasa a matsayin “kasuwa mai mahimmanci”, yana mai cewa babu adadin kudin da aka kashe akanta da yayi yawa.
Comments 1