By Abbas Yakubu Yaura
Wani kwararren lauya mai zaman kansa a garin Lafia Barista Ayiwulu Baba Ayiwulu ya roki mahukuntan a Kwalejin fasaha ta Isa Mustapha Agwai (IMAP) dake Lafia a jihar da su binciki wani al’amari dake faruwa na wasu dabi’u na Allah wadai da wasu daga cikin malamai kan ai kata ga daliban su.
Barista Ayiwulu ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da jaridar Vanguard ta yi dashi inda yayi zargin cewa yanzu haka akwai wasu ‘yan uwansa uku da ke karatu a wannan makarantar baya gasu akwai sauran dalibai wadanda suma sun bayyana damuwarsu dan gane da wannan halayya da wasu daga cikin malaman Kwalejin fasaha suke yi na karbar kudade a hannun daliban.
Baristan yace akwai wasu lakcarorin a cikin wannan Kwalejin wanda mallakin gwamnatin jiha ce suke bukata kowannen dalibi ya basu kudi daga naira 1,000 zuwa abinda yayi sama domin dalibin ya bayar da wani assignment ko kuma su karbi assignment din to sai sun biya naira 1,000.
“Batun karbar kudi a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Nasarawa ya yi yawa a bude. Ka yi tunanin wani malami a cikin aji zai gaya wa ɗalibai su ba da aikin su na (assignment) tare da ₦ 1,000.
“Mafi muni kuma shine lokacin da za a ce dalibai su nemo rubutun jarabawar da suka yi da kansu ko kuma a ce su biya saboda rubutun (script) din nasu ya bata.
“Ina fata hukumar gudanarwar makarantar za ta kafa kwamiti kan wannan batu tare da yin Binciken sirri kan wannan kuma zai taimaka,” a cewar Ayiwulu.
Ayiwulu ya yi zargin cewa biyu daga cikin ’ya’yansa daliban kwalejin kimiyya da fasaha sun fuskanci cin zarafi, duk da cewa binciken ya nuna yadda ake samun karbuwa a makarantar.
Ya kuma yi zargin cewa wasu masu ruwa da tsaki sun bayyana takaicin yadda Malaman Kwalejin fasaha ke karbar dalibai a kan dandali daban-daban.
A saboda haka Ayiwulu ya bukaci hukumar makarantar da ta dauki matakin gaggawa wajen lalubo bakin zaren warware wannan matsala domin kaucewa mummunar akida da take haifarwa a makarantar.
Da yake mayar da martani, jami’in hulda da jama’a na kwalejin kimiyya da fasaha ta Nasarawa, Ali Alhassan wanda ya zanta da manema labarai ya musanta zargin yana mai cewa “ba mu da irin wadannan malamai a makarantar”.
PRO ya yi barazanar cewa hukumar makarantar ba za ta yi kasa a gwiwa ba kan zargin karbar kudi da ake yi da nufin bata sunan makarantar.