Wasu ‘yan bindiga da ake zargin’ yan kungiyar IPOB ne sun cinnawa fadar sarkin gargajiya na al’ummar Etekwuru dake karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar Imo wuta.
Haka kuma an kona motarsa ta kashin kansa, wato wata babbar mota kirar jeep, da sauran kadarori sa yayin harin.
Rahotanni sun ce, lamarin ya faru ne a daren jiya Alhamis.
Biyo bayan gurfanar da Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB a ranar Alhamis, mambobin haramtacciyar kungiyar sun shiga tasku a yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun Cafke Mutane 3 da zargin Tono Gawa a Ogun
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito yadda aka kashe ‘yan ta’addan IPOB da ake zargin sun yi artabu da sojoji a Abia.
Kazalika an kuma kashe wani jami’in soja a wani lamari na daban a jihar ta Imo.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa maharan sun kai farmaki gidan basaraken ne a daren Alhamis.
Sun neme shi cikin tashin hankali, amma tunda ba su same shi ko wani danginsa ba, sai suka cinnawa fadarsa wuta.
A cewar majiyar mu, a halin yanzu basaraken ya samu mafaka a hedikwatar ‘yan sanda da ke Mmahu na jihar.