Kungiyar Masu gidajen wanka da bahaya ta jihar Kano, ta nuna damuwa kan karuwar masu yin bahaya a sarari a kowacce shekara a Najeriya.
Sakataren Kungiyar Alhaji Auwalu Ibrahim shine ya bayyana hakan yayin hirarsa da manema labarai a wani bangare na taron gangamin ranar bandaki ta duniya.
KARANTA ANAN: Dalilin da yasa manufar CBN ta kudi bata aiki – Masanin tattalin arziki
Ya ce jahilci, da riko da tsohuwar al’ada ta wasu daga cikin mutanen Najeriya, da rashin samun wadataccen ruwa don tsaftace makewayi, na daga cikin abubuwan da suke ta’azzara matsalar yin bahaya a sarari a kasar nan.
A cewar sa idan har ana son kawar da matsalar bahaya a sarari a Najeriya, nan da shekaru uku masu zuwa, ana bukatar kudi sama da biliyan 9 da 59 domin dakile illolin da yin bahaya a fili ke haifarwa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa daga cikin illolin sun haɗar da gurbata mahalli ta hanyar iska da ruwa, wanda binciken da asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin UNICEF yayi ya nunar da cewa ana samun mutuwar yara dubu dari 4 da iyaye mata dubu dari sakamakon matsalar yin bahaya a sarari a Najeriya.
A wani labarin kuma: 2023: Mun Yi Shirin Ko Ta Kwana Don Zuwa Zagaye Na Biyu A Zabe – INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce tuni ta fara shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, inda babu wani dan takara da ya cika sharuddan lashe zabe a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Mista Festus Okoye ne ya bayyana hakan a wani taro da shugabannin Kungiyar Editocin yada labarai a ranar Juma’a a Abuja.