Atiku Abubakar dan takarar shugaban Kasa karkashin inuwar jam’iyyar PDP babbar mai hamayya ya ce domin dawo da kasar nan kan turba ana bukatar tuntubar masu ruwa da tsaki na duk bangarorin kasar.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Atiku ya ce yanzu haka yana cibiyar Ecumenical centre domin tattaunawa da kungiyar kiristoci ta kasa CAN a wani bangare na duba yadda za a magance kalubale da matsalolin da kasar ke fuskanta.
KARANTA KUMA Atiku Ya bayyanawa Yan Najeriya Burinsa Idan Ya Zama Shugaban Kasa
Ya ce ya yi alkawarin dawowa da Najeriya hayyacinta tare tattaunawa da bangarori da masu ruwa da tsaki na Kasar.
AA ya bayyana kungiyar Kiristoci a matsayin wani jigo na al’ummar kasar nan da suke da manufar kawo gyara kuma zai zauna da ita kuma a sami gamsuwa.
“Domin dawo da Najeriya kan tsarin muna bukatar tuntubar duk masu ruwa da tsaki a cikin Kasarmu” in ji shi
A cewar AA “Ina Ecumenical Centre da ke Abuja don tattaunawa da kungiyar kiristoci ta Kasa CAN”.
A Wani Labarin Kuma Najeriya Da Kanada Za Su Iya Yin Abubuwa Da Yawa Tare — Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Najeriya da Canada za su iya yin abubuwa da yawa tare ta hanyar inganta kasuwanci, zurfafa hadin gwiwa a fannin ilimi, ci gaba da tattaunawa kan batutuwan sauyin makamashin duniya da sauyin yanayi, da dai sauransu.
Wannan shi ne babban taron da Osinbajo ya yi da mataimakiyar firaministan kasar Canada, Chrystia Freeland, a Ottawa, babban birnin kasar Arewacin Amirka a ranar Litinin.