‘Yan Nijeriya da suka hada da jama’ar gari, kungiyoyi da kuma fitattun mutane na ci gaba da tsanantawa shugaba Buhari tare da sake nanata masa akan da ya kori manyan Hafsoshin rundunonin tsaron kasar, sakamakon yadda matsalar tsaro ke ci gaba da yin muni a kowacce rana a yankin.
Tsohon gwamnan Borno kuma Sanata mai wakiltar yankin tsakiyar jihar Kashim Shettima na daga cikin fitattun mutanen da a baya bayan nan suka nanata bukatar sallamar shugabannin rundunonin tsaron, la’akari da gazawarsu wajen magance matsalolin tsaron dake addabar sassan kasar.
Yayin wata zantawa da kafar talabijin ta Arise, Shettima ya ce kamata ya yi shugaban kasa ya maye guraben manyan hafsoshin tsaron kasar ta mutane masu hikima da sabbin dabarun tunkarar kalubalen da fannin tsaro ke fuskanta gami da kawo karshensa.
A baya-bayan nan ne dai shi ma tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okoracha, ya shawarci shugaba Muhammadu Buhari da ya kori dukkanin mukarrabansa.