Ƴan sanda a jihar Ebonyi sun bayyama cewa suna neman ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar Progressive Grand Alliance(APGA), Ifeanyi Odoh, ruwa a jallo.
Odoh da wasu mutum tara an bayyana ana neman su ne ruwa a jallo a ranar Litinin 6 ga watan Maris, bisa halaka wani basarake mai suna Igbokwe Ewa. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Basu sanya ƙarya ba: Hotunan bikin wasu ma’aurata sun ɗauki hankula sosai
Basaraken dai shine sarkin ƙauyen Umu-Ezekoha a ƙaramar hukumar Ezza ta Arewa wanda wasu ƴan bindiga suka halaka har gida a ranar Litinin da ta gabata.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ebonyi, Onome Onovwakpoyeya, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa:
“Rundunar ƴan sanda jihar Ebonyi tana neman waɗannan mutane ruwa a jallo bisa kisan mai martaba Eze Christopher Igbokwe Ewa, sarkin ƙauyen Umu-Ezekoha a ƙaramar hukumar Ezza ta Arewa.”
Sauran waɗanda ake neman sun haɗa da Samuel Onyekachi Aligwe, Peter Orogwu (wanda akafi sani da one boy),Chukwudi Aliewa (wanda akafi sani da Ezza), Chika Ezealigbo.
Sauran sun haɗa da Nnaemeka Egede (wanda akafi sani da Champaign), Nnabuike Okohu, Ogobuchi Agbom (wanda akafi sani da Okiri), Nonso Obasi, Ikechukwu Nwoba (wanda akafi sani da Solid).
Matasan Rivers Sun Yi Barazanar Kai Kamfanin Shell Ƙara Kotun ICC
Wata kungiyar matasa a yankin Rumuekpe da ke karamar hukumar Emohua a jihar Ribas, ta yi barazanar kai kamfanin samar da man fetur na Shell na Najeriya zuwa kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa.
Sun yi barazanar ne domin neman diyya a sakamakon fashewar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da kona motoci a unguwarsu a ranar Juma’a.