Akalla mutane 33 da suka hada da mata da kananan yara ne aka rawaito sun nutse bayan da wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji sama da 50 ya kife a kogin Kaduna da ke jihar Neja.
Majiyar JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa jirgin ruwan ya kife ne a tsakanin kauyen Danchitagi da ke karamar hukumar Lavun da Gbara da ke karamar hukumar Mokwa a jihar Neja a daren ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin Da Yasa Ilimin ‘Ya’ya Mata Yake Da Muhimmanci – Minista
Majiyoyi da dama sun shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa wasu fasinjojin ’yan kasuwa ne da ke dawowa daga kasuwar Danchitagi ta mako-mako, yayin da wasu kuma ke komawa gida bayan halartar wani daurin aure da aka yi a yankunan makwabta yayin da lamarin ya faru.
An kuma bayyana cewa an yi asarar kayayyakin da suka kai na miliyoyin nairori a wannan mummunan hatsari.
Mazauna kauyen sun shaida wa Daily Trust cewa ya zuwa yanzu an ceto mutane 17 cikin sama da 50 da ke cikin jirgin yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
“A yanzu, cikin fasinjoji sama da 50 da ke cikin wannan kwale-kwalen, mutane 17 ne kawai aka ceto da ransu. Mun yi imanin sauran ba su da rai saboda sun kasance a cikin ruwa na sa’o’i da yawa. Ruwan kuma ya yi yawa a yanzu saboda ruwan sama. Har yanzu muna iyakar kokarinmu don neman sauran mutanen. Amma ba a tabbatar da damar da za su tsira ba, ”in ji daya daga cikin masu ruwa da tsaki na yankin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa lamarin ya faru ne sakamakon ruwan sama mai yawa, tare da tsananin iska.
An ce akasarin wadanda harin ya rutsa da su sun fito ne daga al’ummomin kogin Muregi, Gbara, Gazhe, Tadima da dai sauransu. An kai wasu daga cikin wadanda aka ceto zuwa asibitin karkarar Gbara domin kula da lafiyarsu.
Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Ahmed Ibrahim Inga, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin, sai dai ya ce ba zai iya bayar da cikakken bayani kan asarar rayuka ba.
Ya ce hukumar ta kaddamar da ayyukan ceto da nufin ceto rayukan wadanda lamarin ya shafa.
Hakimin Gbara, Alhaji Mohammed Saba, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce fasinjojin da basu gaza 60 ba ne a cikin kwale-kwalen.
A wani labarin kuma,
Yajin Aikin ASUU: Dalibin Likitaci A Shekarar Karshe Da Ya Fara Sayar Da Abinci Ya Rasu
Malam Usman Abubakar-Rimi, wanda dalibi ne a shekarar karshe a fannin likitanci da tiyata a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto (UDUS), wanda ya tsunduma harkar sayar da abinci saboda yajin aikin ASUU, ya rasu.
Abubakar-Rimi ya bude wani katafaren gidan abinci da taliyar yara sato Indomie a Unguwar Diplomat a Sokoto.