By Abbas Yakubu Yaura
An samu tashin hankali a yankin Lafenwa da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin da ‘yan kabilar Yarbawa da Hausawa suka yi artabu da safiyar yau, wanda ya yi sanadin lalata kadarori da raunata mutane.
Wani ganau mai suna Malam Hassan ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya samo asali ne da safiyar ranar Talata lokacin da wasu ‘yan kabilar Yarbawa suka tare wani Bahaushe a kan hanyar Brewery, kusa da Lafenwa.
Ya ce, “’yan daban sun so karbar kudi daga hannun Bahaushen da karfin tsiya, amma sai ya bijire masa ya fasa masa kwalba a kai, inda suka yi masa rauni. Masu wucewa sun garzaya da shi zuwa asibitoci da dama, amma an ki yarda da akarbe shi kafin daya daga cikin asibitocin ya karbe shi.inda ya rasu da maraice kuma hakan ne ya janyo fada tsakanin Yarabawa da Hausawa masu fataucin Kasuwar Shedi da ke kusa da barikin Lafenwa.
A yanzu haka ana kona kayayyakin dake cikin kasuwannin da ake sayar da su tare da raunata kusan mutane bakwai wasu biyu kuma suka mutu. Maharan sun yi amfani da damar kuma sun shiga shaguna da dama don wawashe dukiyar ‘yan kasuwa. Har ma sun kai hari ofishin ‘yan sanda da ke kusa da titin jirgin kasa, wanda ke kusa da kasuwa.”
Jaridar Dimokuradiyya ta kuma gano cewa Sarkin Abeokuta, Alhaji Ibrahim Hassan ya samu munanan raunuka bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai masa hari da adduna.
Muhammad dan uwan Sarkin Hausawa ya shaida wa wakilinmu cewa an kai wa Sarkin Hausawa hari ne a hanyarsa ta zuwa Lafenwa don shiga tsakani.
“Sarki ya je ya shiga tsakani, amma abin takaici, ‘yan daba sun far masa; An kai shi babban asibiti inda aka ki amincewa da shi, amma daga baya aka kwantar da shi a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Abeokuta,” inji shi.
Mai ba Gwamnan Jihar Ogun shawara na musamman kan harkokin kabilu, Abdulhadi Sani, ya shaida wa Daily Trust cewa an shawo kan lamarin.
Ya ce, “Na kasance a FMC tun safe; Sarkin Hausawa na samun sauki kuma har yanzu muna karbar wadanda lamarin ya rutsa dasu.
Shi ma shugaban karamar hukumar Abeokuta ta Arewa yana nan kuma kwamishinan ‘yan sandan yana wurin da lamarin ya faru.”
Kazalika, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa manema labarai cewa al’amarin ya gudana, kuma ‘yan sanda na binciken lamarin.
“Ba zan iya ba ku alkaluman wadanda abin ya rutsa da su ba da wadanda suka rasa rayukansu ba saboda har yanzu muna kan bincike lamarin. Zan dawo muku da cikakken bayani,” inji shi.
Wakilinmu ya samu labarin cewa Jami’an tsaro sun kulle Kasuwar Shedi.