Wata mata wacce take lalata da wani mutum an gano cewa matar aure ce kuma wani fasto take aure a yankin, Nigerian Pulse ta ruwaito.
Bokan wanda har yanzu ba a gano shi, ya fadi ya mutu yana tsaka da gwada kwazonsa da matar a wani otal da ke Ikere Ekiti, hedkwatar karamar hukumar Ikere da ke Jihar Ekiti.
KU KARANTA: Budurwa ta faɗa tarkon soyayyar boka, ta wallafa bidiyonsu suna soyayya
Lamarin ya auku ne ranar Litinin, 2 ga watan Janairun 2023 yayin da mai maganin gargajiyan ya hadu da matar a otal.
A cewar ganau, wanda ya sha mamakin lamarin, ya ce matar wani fasto ce a daya daga cikin cocinan yankin inda abin ya faru.
“Mutumin ya mutu ne a dakin otal yayin lalata da matar. Ta bayyana hakan ne bayan ganin mutimin ya fadi ya mutu.”
Manajan otal din da sauran mazauna yankin sun yi gaggawar zuwa wurin inda suka kai shi asibitin kusa da otal din inda aka tabbatar ya mutu.
Ina zargin mutumin ya yi mata asiri ne. Yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan Oyo, Sunday Abutu ya ce jami’an yanzu haka sun fara bincike kan dalilin mutuwarsa.
Ya ce sai an tabbatar an dauki hukuncin da ya dace a kan lamarin.
Kano: An Cafke Wani Boka Dake Dubgawa Matan Mutane Ciki Da Sunan Taimako
Daga jihar Kano rahotonni ne suka bayyana, dangane da yadda aka kama Wani Boka da ake Zargin sa Yana lalata da Mata, da sunan zai cire musu Aljani, da kuma basu Maganin korar Kishiya.
Hukumar hisbah ta karamar hukumar Dawakin Kudu, karkashin jagorancin Ustazu Kabiru Musa Dawakiji ta kama bokan Mai suna Muhammad Mansur, ne a garin Kode.
Rahotanni suna bayyana cewa Boka Mansir ya dade yana ribatar su ta wannan hanya, dacewa zai basu tallafin maganin mallakar miji ko dai na biyan wasu bukatun su.