Fadar shugaban kasa ta yi zargin wadansu ‘gurbatattun’ ‘yan siyasa da suke aiki tukuru wajen ganin sun bata wa shugaban kasa da ofishinsa suna. Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Laraba.
Inda ya kara da cewa; wadannan mutanen suna amfani da shafukan sada zumunta da kafafen watsa labaran dake Intanet wajen cimma “mummunan manufofinsu” inji Adesina. A cewarsa, manufar shi ne a kwanakin da za a fuskanta za a kaddamar da kamfen din bata wa shugaban kasar suna, inda za a nuna cewa shugaban kasar ba shi ne yake jan ragamar shugabancin kasar ba.
Inda ya ce tuni ma dama aka fara yada irin wannan da’awar.