Wasu ‘yan jihar Kano karkashin kungiyar ci gaban Darmanawa Layout, na zargin asusun lamunin birnin Ado Bayero, wani asusun masarautar Kano, da yunkurin kwace filin Idi da kuma sayar da shi.
Shugaban kwamitin filin Idi, Barista Tijjani Yahaya, ya bayyanawa manema labarai a jihar Kano cewa Marigayi Ado Bayero ne ya bayar da filin kyauta ga garin kuma gwamnatin jihar ta tabbatar da hakan. Tijjani Yahaya ya bayyana cewa irin haka ya taba faruwa a 2019 lokacin wasu suka yi kokarin sayar da filin.
A cewarsa, Filin ita ce wajen Sallan idi daya tilo dake karamar hukumar Tarauni gaba daya. Shugaban kungiyar ya kara da cewa sun rubuta wasika ga hukumar korafe-korafe da yaki da rashawa na jihar Kano a Oktoban 2020, domin hana masarautar kwace filin. Yayin da muke sauraron sakamakon wadannan kararraki da muka shigar, wakilan asusun lamunin birnin Ado Bayero sun yi kokarin kwace filin karfi da yaji kuma mun samu nasaran hana su a 30 ga Disamban, 2020.
Ya ce saboda haka, muna kira ga asusun lamunin Ado Bayero ta gabatar wani hujja dake nuna cewa filinta ne.