Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da mutane takwas a wasu kananan hukumomi biyu na jihar Kaduna.
Majiyoyin Dimokuradiyya sun ce maharan sun mamaye kauyen Autan Kuli da ke unguwar Yakawada a karamar hukumar Giwa inda suka yi awon gaba da mutane shida.
Wani mazaunin yankin da ya so a sakaya sunansa ya ce, “’yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 2 na rana a ranar Alhamis din nan, inda suka rika harbin iska.
KU KARANTA KUMA: An Yi Garkuwa Da Tsohon Sakataren Gwamnati Jiha
“Duk da haka sun yi nasarar yin garkuwa da mutane shida: Usman mai Unguwa, Mashakuru Audu, Umma Nasiru, Hauwa Nasiru, Jamilu umar, da Sunusi Bashari.”
A wani lamari makamancin haka, an yi garkuwa da mutane biyu a Hayin Mallam da ke unguwar Jama’a a karamar hukumar Sabon Gari a ranar Laraba.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Wata majiyar ‘yan banga ta ce, “da misalin karfe 11:30 na daren ranar Laraba, masu garkuwa da mutane sun shiga wani gida a kan titin Shaka suka yi garkuwa da mutane biyu.”
A cewar majiyar, “Wadanda aka yi garkuwa da su sune Musa Omeza da Fatima Hassan bayan harbe-harbe da aka yi.”
Ya kara da cewa “Bayan faruwar lamarin, ‘yan kungiyar ‘yan banga sun je aikin ceto amma ba su samu nasarar gano bata garinba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalinge, bai amsa kiran da wakilinmu ya yi masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
A Wani Labarin Kuma: Karin Kasashe Hudu Sun Sanar Da Faɗakarwar Ta’addanci A Najeriya
Gwamnatocin kasashen Jamus da Bulgeriya da Ireland da kuma Denmark sun gargadi ‘yan kasarsu kan tafiye-tafiye marasa mahimmanci zuwa Abuja, babban birnin tarayyar kasar nan saboda karuwar hare-haren ta’addanci.
Shawarwarin tafiye-tafiyen ya zo ne kwanaki kadan bayan Amurka, Birtaniya, Australia da Kanada sun yi gargadin yiwuwar kai harin ta’addanci a Abuja.