An sace tsohon sakataren gwamnatin jihar Enugu, Dr. Dan Shere.
Majiyar JARIDAR DIMOKURADIYYA ta samu labarin cewa yana cikin wasu matafiya da aka yi garkuwa da su a hanyar Enugu-Ugwuogo Nike-Nsukka ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Sanda Sun Damke Wani Mutum Dauke Da Katunan Zabe Guda 101 A Sokoto
Shere, wanda ya kasance likita ne,kuma ya yi aiki a karkashin gwamnatin tsohon Gwamna Chimaroke Nnamani.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa dan siyasar na Enugu yana tafiya Nsukka ne domin ganawa da ‘yan bindigar tare da wasu matafiya.
Daya daga cikin wadanda suka tsira da ransu, wanda ya yada hoton bidiyon harin, ya ce ‘yan bindigar sun kai su kimanin takwas.
“Sun harbi motar mu da yawa; daya daga cikin mu harsashi ya same shi. Amma direbanmu ya ci gaba da tafiya, Mun yi nasarar kai wanda abin ya shafa zuwa asibiti.” Inji shi yayin da yake gode wa Allah da ya cece shi da wasu mutane hudu daga al’umma daya.
A halin da ake ciki, an tattaro cewa masu garkuwa da mutane wadanda aka ce Fulani makiyaya ne, sun kara neman kudin fansa kan wadanda suka karba tun farko a ranar Lahadi.
“Tun da farko sun bukaci daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya biya su Naira 2 amma yanzu sun kara zuwa Naira miliyan 30m. Suna bincika wayoyin wadanda abin ya shafa domin sanin halin da suke ciki,” inji majiyar.
Har yanzu dai ba a sako daliban jami’ar Nsukka da aka dawo da su a ranar Lahadin da ta gabata ba.
Ba a mayar da binciken da aka aika ga jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, DSP Daniel Ndukwe har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba.
A wani labarin kuma, Kasar Ukraine Ta Dakatar Da Tattaunawar Zaman Lafiya Kan Umarnin Amurka — Kremlin
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi ikirarin cewa Ukraine ta fice daga tattaunawar zaman lafiya da Moscow a watan Maris kan “umarni” daga kasar Amurka, in ji Kremlin a ranar Alhamis.
Kakakin Kremlin, Dmitry Peskov, ya shaida wa manema labarai cewa, “Rubutun ya shirya, sa’an nan kuma ba zato ba tsammani bangaren Ukraine ya fita daga tattaunawar, saboda bangaren Ukraine ya bayyana rashin son ci gaba da tattaunawa,” in ji mai magana da yawun Kremlin, Dmitry Peskov.