Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti, ya bayyana tsohon dan wasan Manchester City Edin Dzeko da tsohon dan wasan gaba na Paris Saint-Germain Mauro Icardi a matsayin ‘yan wasan da zai dauka don karfafa gwiwar kungiyarsa.
A cewar El Nacional, Ancelotti yana so ya kawo Dzeko da Icardi zuwa Real Madrid don ƙarfafa kai hari, saboda Karim Benzema yana fama da rauni.
KU KARANTA: NLC Ta Bukaci Buhari Ya Tsoma Baki Don Sakin Hakkokin Malaman ASUU
Benzema ya buga wa Real Madrid wasanni 19 kacal a kakar wasa ta bana inda ya zura kwallaye 13 sannan ya taimaka wajen cin wasa daya.
Haka kuma Real Madrid tana da ‘yan wasa irin su Vinicius Jr. da Rodrygo a cikin ta. Duk da haka, babu wani wanda zai maye gurbin Benzema kai tsaye, saboda rashin kyawun yanayin Eden Hazard bai sanya al’amura su yi sauki ga Ancelotti a Santiago Bernabeu ba.
Don haka, Ancelotti yana binciko yan wasa masu kyau don karfafawa kungiyarsa gwiwa wajen kai hari a sauran kakar wasa.
A halin yanzu Real Madrid ce ta biyu a teburin gasar La Liga yayin da take neman kare matsayinta a jerin zakarun Spain.
A wani labarin kuma: Da Kan Ku Zaku Gode Mun Nan Gaba Kan Sauyin Kuɗin – Martanin Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Asabar ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa ‘yan kasa ba su samu wata matsala a harkokin kasuwancin su ba, daidai lokacin da ake ci gaba da samun damuwa kan batun daina karbar wasu daga cikin tsofaffin kudi a Najeriya.
Buhari kuma ya ce ba za a samu cikas ga daukacin hanyoyin samar da kayayyaki ga al’umma ba, duk kuwa da irin halin da ake shiga wajen musayar kudaden da za a kawo karshe amfani da su nan ba da dadewa.