Wata mata ta bayyana yadda ta yi babbar kofa wacce za ta Lange diyarta mai shekaru 5 daga shiga kicin dinta saboda yawan cin abinci, Dailymail ta ruwaito.
KU KARANTA: Wata ta yi kaciɓus da mijinta wurin cin abinci duk da ya mutu shekaru 9 baya
Likitoci sun gano diyar Holly Williams, Harlow tana fama da wata cuta tun lokacin tana da watanni 6 a duniya.
Wannan cutar da ke damun Harlow tana sanya ta jin yunwa a kowane lokaci don haka ba ta koshi.
Matar mai shekaru 25 daga Newport a Wales sai da ta koma a kowane lokaci tana boye abinci har ta kai ga ta sanya katon kwado a kofar kicin din yayin da diyarta ta girma.
Kamar yadda ta bayyana:
“Samun kofar yara a bakin kofa ta taimaka min wurin dakatar da Harlow daga zuwa wurin durowoyin kicin don samo wa kanta abinci.
“Sakamakon halin da take ciki, Harlow tana da nauyin 44lbs wanda ya zarce nauyin ‘yar shekara 5.”
Yayin da ta bayyana yadda lamarin ya taba rayuwarta kwarai, Holly ta cigaba da cewa:
“Tana cin abinci a koyaushe kuma tana kammalawa take cewa tana jin yunwa.
Wata Sabuwa: Saurayi Ya Rabu Da Budurwarsa Kan Rashin Iya Abinci Mai Daɗi
Hirar da suka yi a manhajar Whatsapp wacce ta nuna yadda suka rabu kowa ya kama gabansa, wani amfani da @JNRdeyforyou ya sanya ta a Twitter. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Vivian ta kai wa Josh ziyara a gida lokacin baya nan, inda ta gaya masa a WhatsApp cewa tayi niyyar tayi masa girki.