Hakimin Ɗan Batta, kuma Sarkin Ban Bichi, Alhaji Isiyaku Wada Waziri ya buƙaci gwamnatin Kano ta mayar da GSS Dambatta kwalejin ilimi domin saukakawa mutanen yankin zuwa makarantar gaba da sakandare.
Hakimin na wannan kira ne a taron raba tallafi ga mata da matasa a karamar hukumar Danbatta.
Yace hakan zai taimakawa ci gaban ilimi a yankin baki daya, sakamakon yadda Dalibai ke Shan wahala wajen zuwa karatu a wasu daga cikin manyan makarantun gaba da sikandire.
Da yake jawabi tun da fari, Hakimin Makoda, Barayan Bichi, Labaran Abdullahi ya ce akwai buƙatar ƴan siyasa su zama masu hadin kai domin ci gaban al’umma.
Ya ce ta haka ne kawai mutane za su mori shugabanci a yankunan nasu.
Dukkanin hakiman sun yaba da bayar da tallafi ga mata da matasan yankin, wanda a cewar su akwai bukatar ci gaba da tallafawa mutane domin rage musu Halin da suke ciki.