Jam’iyyar APC Mai Miki ta kasa, ta bayyana ranar 4 ga watan Satumba shekarar 2021, a matsayin ranar da za ta gudanar da babban taronta na jihohi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nasarawa ta Kori Dalibai 51
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata ta-kaitacciyar takaddar sanar wa da jam’iyar ta fitar, Wanda tai wa take da: “Jam’iyar APC ta bayyana 4 ga watan Satumban 2021, a matsayin ranar da za ta gudanar da gaggamin ta, a kananan hukumomi; kuma amfara Saida Fom Mai dauke da sa hannun Babban sakataren jam’iyar na kasa wato Sanata John Akpanidoedehe, a yau Laraba, a garin Abuja” inji sanar war.
Cikakkun bayanai
A wani labarin Kuma na daban.
Yanda muka magance Yan ta’addan Boko Haram daga Shigowa Jami’ar UNIMAID, inji Tsohon VC
Tsohon Shugaban Jami’ar Maiduguri dake Jahar Borno Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bayyana yadda Makarantar ta hana Yan ta’addan Boko Haram daga Shigowa cikin ta.
Njodi Wanda shine Sakataren Gwamnatin Jahar Gombe, ya bayyana haka a wata Lakca da Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Kashere ta Shirya dake Jahar Gombe.
Lakcar Mai taken “Jami’o’i a lokacin Yan ta’adda: yanayin da Jami’ar Maiduguri ta fuskanta a lokacin Boko Haram.
Tsohon Shugaban Jami’ar Maiduguri yace, daya daga cikin matakan da Jami’ar ta ajiye domin magance wa Jami’ar shigowar Yan ta’addan Boko Haram shine tafiya da kowa da kowa.
Farfesa Njodi ya kara dacewa, sun kuma shigo da Jami’an tsaro da suka hada da Yansanda, DSS, Sojoji da sauran su, domin karawa masu kula da makarantar karfi domin samun tsaro a Jami’ar.
Ya bayyana cewa, Jami’ar ta kuma sanya jindadin Dalibai a matsayin abinda ta sanya a gaba, ta hanyar ziyartar su lokaci-lokaci zuwa Dakunan Kwanan su, wannan ya taimaka kwara dagaske.
Ya kuma bada tabbacin kudirin sa na inganta harkokin karatu da Cigaban Makarantar ta Kashere, da Malaman ta da Dalibai da inganta jindadin su.
Comments 1