Baban Yar tsohon gwamnan jihar Yobe Bukar Abba Ibrahim ta rasu.
Marigayya Aisha ta rasu ne da sanyin safiyar yau Laraba, a wani asibiti dake Cairo babban birnin kasar Masar, bayan ta yi fama da matsanan cin rashin lafiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: APC ta bayyana ranar da za ta yi Taron gaggamin ta
Yanzu haka ana kan gudanar da Jana’Izarta ne a birnin Cairo, ya yin da aka shirya amsan ta’aziya a gidan Mahaifinta wato Bukar Abba Ibrahim, dake gini mai lamba 13A kan hanyar Owena close, kusa da hanyar Yedseram na yankin Maitama, a babban birnin tarayya Abuja.
Kazalika iyalanta sun bayyana cewa, za’a sanar da sauran shirye shiryen addu’ar 3 da na 7, nan ba da jima wa ba.
A wani labarin Kuma na daban.
Jamhuriyar Nijar ta bada hutun kwana biyu domin zaman makoki na mutane 37 da Yan ta’adda suka kashe a Kasar
Jamhuriyar Nijar a ranar ranar Laraba ta bada hutun awanni 48 domin jimami tare da zaman makoki akan kisan mutane 37, da ake kyauta ta zaton Yan Jihadi suka aikata mummunan aikin.
“An Kuma bada umarnin jawo tutocin Kasar ya zuwa kasa-kasa, Wanda umarnin ya fara nan take, kamar yadda Sanarwar Gwamnati ta bayyana.
Sanarwar tace Gwamnatin a shirye take domin yaki da ta’addanci har sai an kawo shi a matakin karshe.
Yan ta’adda a saman Babura suka kai harin a ranar Litinin a Kauyen Darey-Darey, inda Mata da Kananan yara 13 suka kashe daga cikin 37.
Garin Darey-Darey, sun taba kai mashi Hari a watan Maris, inda suka kashe mutane 66.