APC ta caccaki Gwamnan Rivers kan gabatar da kasafin kudi ga ƴan majalisa hudu
Jam’iyyar APC, ta caccaki Gwamna Siminalayi Fubara da ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 ga mambobin majalisar dokokin jihar hudu cikin 31.
A ranar Laraba ne Fubara ya gabatar da kasafin Naira biliyan 800 na shekarar 2024 ga ‘yan majalisar guda hudu da ake kyautata zaton suna masa biyayya a gidan gwamnati da ke Fatakwal, ‘yan mintoci kadan bayan ruguje harabar majalisar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Ɗuminsa: Babban Lauyan Jihar Ribas yayi murabus
Sai dai Mista Tony Okocha, shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC na jihar, ya bayyana a wata sanarwa a Fatakwal cewa matakin ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.
Okocha ya ce sashe na 120(2) na kundin tsarin mulkin kasar ya bayyana karara cewa babu wani kudi da za a kashe sai dai majalisar dokokin jihar ta ware.
‘’ Gabatar da kudirin doka ga ‘yan majalisar 4 da aka dakatar bai cika ka’idojin tsarin mulki ba saboda duk dalilan da aka bayyana.
Okocha ya yi gargadin cewa kashe kudi da gwamnatin jihar ta yi kan sakamakon irin wannan gabatar da kara ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar, don haka ne ma ya isa ya isa a tsige shi.
Ya kuma ce sashe na 92(2)C ya tanadi cewa za a iya tsige shugaban majalisar da kashi biyu bisa uku na majalisar.
Okocha ya yi zargin cewa babu wata shaida da ta nuna cewa an tsige Mista Martins Amaewhule, shugaban majalisar daga mukaminsa.
‘’Amaewhule ya kasance shugaban majalisar, ‘yan majalisar sun kada kuri’ar amincewa da shi,’’ inji shi.
A wani labarin kuma:Za mu ɗage takunkumin da muka sanyawa Nijar idan suna so – ECOWAS
Mista Sidie Tunis, Shugaban Majalisar ECOWAS, ya ce za a dakatar da hukuncin da aka yanke wa Jamhuriyar Nijar, idan har gwamnatin soja ta saki Shugaba Mohamed Bazoum.
Shugaban majalisar ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da tawagar mutane 19 daga kungiyar ‘yan Afrikan da ba su da iyaka suka kai masa ziyarar ban girma a Abuja.