Kotu ta ɗaure mutumin da ya amsa laifin satar mota
Wata Kotun Majistare ta Badagry da ke Legas, a ranar Alhamis, ta bayar da umarnin a tsare wani mutum mai shekaru 52, Charles Ogaba saboda ya amsa laifin satar mota.
Alkalin kotun, Fadahunsi Adefioye ya bayar da umarnin tsare Ogaba bayan ya amsa laifuka biyu da suka hada da sata da canza fasalin ta.
KARANTA WANNAN LABARIN:Za mu ɗage takunkumin da muka sanyawa Nijar idan suna so – ECOWAS
Adefioye ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali na Awhajigoh, Badagry, sannan ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 21 ga watan Disamba domin samun hujjoji da kuma yanke hukunci.
Tun da farko mai gabatar da kara, Clement Okuoimose, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Yuli da misalin karfe 1.00. pm, a unguwar Ibereko a Badagry, Legas.
A cewar mai gabatar da kara, wanda ake tuhumar ya saci mota kirar Toyota Sienna 2000 mai lamba FST 955 PT wacce kudinta ya kai N1.4m, mallakin Ogala Adeku, wanda ya kai karar.
Ya kara da cewa wanda ake karar ya canza kudi naira 700,000 wanda kudin motar ne ba tare da izinin mai shi ba, yana mai jaddada cewa laifin ya saba wa sashe na 287 na dokar laifuka ta jihar Legas, 2015.
A wani labarin kuma:APC ta caccaki Gwamnan Rivers kan gabatar da kasafin kudi ga ƴan majalisa hudu
Jam’iyyar APC, ta caccaki Gwamna Siminalayi Fubara da ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 ga mambobin majalisar dokokin jihar hudu cikin 31.
A ranar Laraba ne Fubara ya gabatar da kasafin Naira biliyan 800 na shekarar 2024 ga ‘yan majalisar guda hudu da ake kyautata zaton suna masa biyayya a gidan gwamnati da ke Fatakwal, ‘yan mintoci kadan bayan ruguje harabar majalisar.