Jam’iyyar APC a ranar juma’a ta fara gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar domin zabar wanda zai tsaya mata takarar gwamnan jihar Bayelsa da aka shirya gudanarwa a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Da yake jawabi ga manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta jihar da ke Yenagoa, jim kadan bayan kammala wani taro da jiga-jigan jam’iyyar da ‘yan takara, shugaban kwamitin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, Manjo Janar A. T. Jibrin, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta amince da zabin A4 a zaben fidda gwanin da ake sa ran za a yi na kato bayan kato a duk mazabu 105 na jihar,kamar yadda Vanguard ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano Da Kaduna – TCN
Ya yi nuni da cewa, an kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da atisayen ba tare da tangarda ba, ya kuma ba da tabbacin jam’iyyar ta amince da gudanar da zaben fidda gwani na gaskiya da lumana a jihar.
Jibrin wanda ke tare da shugaban kwamitin daukaka kara na zaben fidda gwani DIG Habila Joshua da sauran mambobin kwamitocin biyu, ya ce an wanke ‘yan takara shida a zaben fidda gwani.
Mutanen shida da suka nemi takarar sun hada da tsohon karamin ministan man fetur, kuma tsohon gwamnan jihar, Cif Timipre Sylva, zababben gwamnan jihar a 2019, Cif David Pereworimini Lyon, Festus Daumiebi Sunday, Farfesa Ongoebi Etebu Maureen, Ogomade Isikima Johnson, da kuma Joshua Maciver.
Ya ce: “Kwamitin ya yi tattaunawa da jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Rundunar ‘yan sandan Bayelsa, da Hukumar Tsaro ta farin kaya, DSS da kuma Hukumar Tsaro NSCDC, domin neman shawarar yadda za a gudanar da atisayen cikin lumana bisa ka’ida.
“Ba za mu iya bayar da jimillar alkaluman ‘ya’yan jam’iyyar ba, domin a wasu unguwannin, kuna da mutum 100, a wasu kuma kadan ne. Don haka yana da wahala saboda akwai mazabu 105, yana da wahala a cire shi daga saman kaina. Amma ku sani muna da rajista ga duk wanda zai shiga. Za mu ba kowa izini kafin ya kada kuri’arsa.
“Muna ba da tabbacin gudanar da rijistar masu kada kuri’a bisa rajistar jam’iyyarmu a kowace shiyya da ke kananan hukumomi takwas kuma ba za a bari kowa ya shiga jerin masu kada kuri’a ba har sai an tabbatar da shi.”
Mambobin kwamitin zaben fidda gwani na karkashin jagorancin shugaban kungiyar Manjo Janar AT Jibrin, sauran mambobin kwamitin sun hada da Adejoh Seer, sakatare, Dr Ndubusi Agbo, Muhanned Diwar, Abdulmalik Mohammed, Mr Opemipo Olorunfemi da Hon Titi oseni.
A wani labarin kuma, Yadda APC da PDP Suka Bazama Don Lashe Zaben Gobe Asabar
Manyan jamiyyun kasar nan APC da PDP sun shiga daura damarar samun nasarar lashe zabukan da basu kammala ba na gwamnan da kuma yan majalisun dokoki a sassa daban daban na kasar nan.
Yanzu haka dai akwai kujeru yan majalisun tarayya da na jihohi 93 da za a sake wani zabe a akwatuna daban daban daga wasu mazabun kananan hukumomi a kasar nan.