Yanzu haka dai mambobin jam’iyyar APC na jihar Kogi, a yau juma’a za su fito domin zaben dan takarar gwamnan jam’iyyar ta hanyar zaben fidda gwani na kato bayan kato.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito da yake jawabi ga ‘ya’yan jam’iyyar a taron masu ruwa da tsaki da aka yi jiya, Shugaban Kwamitin taron kuma Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle ya ce wadanda sunayensu ke cikin rajista ne kadai za a ba su damar kada kuri’a.
KARANTA WANNAN LABARIN:APC Ta Fara Zaben Fidda Gwani Kai Tsaye Domin Zabar Dan Takarar Gwamna
Manyan wadanda zasu fafata a zaben fidda gwani su ne Barista Salami Ozigi Deedat, Hon.Usman Ododo, Dr. Sanusi Ohiare, Sanata Smart Adeyemi da Farfesa Stephen Ocheni.
Ku tuna cewa mataimakin gwamnan jihar Kogi, Cif Edward Onoja a ranar Alhamis ya janye daga takarar gwamnan jihar Kogi.
Tsohon Akanta Janar Jibrin Momoh da kuma Asiru Idris tsohon kwamishinan kudi, kasafin kudi da tsare-tsare sun janye daga takarar.
Banji jimoh, Muhammad Jamiu Asuku, Friday Idachaba da Hajia Halima Alfa suma sun janye daga takarar.
Sanarwar ficewar tasu ta fito ne daga bakin babban jami’i mai kula da zaben fidda gwani na gwamnan APC, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.
A wani labarin kuma, Dalilin Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano Da Kaduna – TCN
Kamfanin raba hasken wutar na kasa TCN, ya danganta rashin wutar lantarkin da ake fama da ita a jihar Kano sakamakon gazawar kamfanin wajen gyara wasu layukan tunkuda wutar, a daya daga cikin layin kamfanin mai karfin 330KVA da ke baiwa jihohin Kaduna da Kano, sakamakon ayyukan ‘yan bindiga a dajin Birnin Gwari.
Babban Manajan kamfanin TCN a yankin Kano Alh. Bashir Muhammad Gote a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano, ya ce samun maatsalar da layukan suka yi, ya taimaka wajen shigar da jama’a da dama cikin wahala. Daily reporters24 ta rawaito.