- Jam’iyyar APC ta karyata rahotannin da ke cewa ta gabatar dan uwan tsohon Gwamna David Umahi, Austin, domin maye gurbinsa a majalisar dattawa
- Kujerar Dan majalisar dattawan ta kasance babu kowa bayan Sanata mai ci ya zama minista
- APC za ta tsayar da dan takarar da zai maye gurbin kujerar nan bada jimawa ba
Jam’iyyar APC a jihar Ebonyi, ta karyata rahotannin da ke cewa ta gabatar dan uwan tsohon Gwamna David Umahi, Austin, domin maye gurbinsa a majalisar dattawa, Daily Post ta rawaito.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa kujerar Dan majalisar dattawan Ebonyi ta kudu ta zama babu kowa bayan da Sanata Umahi ya zama ministan ayyuka.
KARANTA WANNAN: Gwamna Fubara Ya Ba da Gudummawar Motar Kashe Gobara ga FAAN
Shugaban jam’iyyar na jihar, Stanley Okoro-Emegha, ya karyata rahoton a ranar Litinin a Abakaliki yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce rahoton ‘karya ne’.
Okoro-Emegha ya ce ba a tantance Austin ko wani mutum da zai cike gurbin ba, domin jam’iyyar za ta sake gudanar da wani sabon zaben fidda gwanin dan takara.
“APC za ta tsayar da dan takarar da zai rike kujerar saboda tamu ce.
“Ba za mu bari duk wata kujera ta jam’iyyar ta tafi zuwa ga wata jam’iyyar adawa ba saboda muna kan kasa a jihar,” in ji shi.
Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani domin zabar dan takarar da zai samu karbuwa a wajenta da al’umma.
“Kujerar zaɓe ce, don haka ya kamata wanda ke zaune a cikinta ya fito ta hanyar gaskiya ba ta hanyar kakabe ba.
“Gwamna a matsayinsa na shugaban jam’iyyar yana da ‘yancin marawa duk wani mai son tsayawa takara baya, amma hakan ba ya nufin cewa tikitin na kowa ba ne,” in ji shi.
Ya yi nuni da cewa jam’iyyar tana jiran hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da kujerun a matsayin wadda babu kowa tare da fitar da ka’idojin yadda za a gudanar da zaben ta.
“Wadanda kuma suke cewa za mu rasa kujerar gwamnan jihar a kotun, suna yin mafarki ne saboda an same ta ne ta hanyar gagarumin aiki.
“Gwamnan ta hanyar manufofinsa, ya fara tabbatar da amincewar da jama’a suka yi masa, saboda sun san iya karfinsa kafin zabensa,” inji shi.
A wani labarin kuma, Kakakin Jam’iyyar PDP Ya Yi Murabus
Mai magana da yawun jam’iyyar PDP na jihar Kwara Prince Tunji Moronfoye ya yi murabus daga mukaminsa
Cigaban na kunshe ne a cikin wata takarda da ya aikewa shugaban jam’iyyar na jiha
Sakataren yada labaran yace yayi murabus dinne bisa wasu dalilai na kashin kai
Prince Tunji Moronfoye, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP a Jihar Kwara ya yi murabus daga mukaminsa.
Cigaban na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan 04/09/2023 kuma aka aika zuwa ga shugaban jam’iyyar na jiha, Babatunde Muhammed.