- Mai magana da yawun jam’iyyar PDP na jihar Kwara Prince Tunji Moronfoye ya yi murabus daga mukaminsa
- Cigaban na kunshe ne a cikin wata takarda da ya aikewa shugaban jam’iyyar na jiha
- Sakataren yada labaran yace yayi murabus dinne bisa wasu dalilai na kashin kai
Prince Tunji Moronfoye, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP a Jihar Kwara ya yi murabus daga mukaminsa, Daily Post ta rawaito.
Cigaban na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan 04/09/2023 kuma aka aika zuwa ga shugaban jam’iyyar na jiha, Babatunde Muhammed.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: NLC ta Yi Fatali da Ganawa da FG kan Tsunduma Yajin Aiki
Prince Tunji ya ce “Na rubuto muku wannan wasika ne domin nuna niyyata ta yin murabus daga mukamina na sakataren yada labarai na jam’iyyar da kuma wakilin kwamitin gudanarwa na jiha SWC.
Ya ce ya yanke shawarar ne bisa wasu dalilai na kashin kai kuma “Ba ni da kiyayya ga jam’iyyar PDP da kuma shugabannin ta na kasa Sir.
Ya kara da cewa, “abin girmamawa ne kuma gata ne yin aiki tare da babbar kungiya kuma zan iya yaba wa dukkan wakilan SWC da na yi aiki da su, a lokacin da na rike ofis,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Zulum Zai dasa Bishiyu Miliyan 10 Don Maye Gurbin Wadanda Tashe-Tashen Hankula Ya Kawar
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya kuduri aniyar dasa bishiyu miliyan 10 domin maye gurbin bishiyun da aka yi asararsu sakamakon tashe-tashen hankula
Gwamnan yace galibin bishiyun da ke kewayen kauyukan jihar an cire su ne saboda dalilai na tsaro
Amfani da bishiyu wajen sare su don yin makashin abinci ya taimaka wajen samun karancin bishiyu a jihar
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kuduri aniyar dasa bishiyu miliyan 10 domin maye gurbin kashi 80% na bishiyun da aka yi asararsu sakamakon tashe-tashen hankula a jihar.
Da yake magana a ranar Litinin a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Borno da ke Maiduguri a yayin kaddamar da gangamin yakin neman zabe na shekarar 2023, inda ake sa ran za a dasa bishiyu miliyan 1.2 a fadin jihar, Zulum ya bayyana cewa, gangamin na da nufin dakile kwararowar hamada da sauran matsalolin muhalli a yankunan jihar.
Ya yi nuni da cewa, galibin bishiyun da ke kewayen kauyukan jihar an cire su ne saboda dalilai na tsaro, wasu kuma an sare su ne saboda itace.