Jam’iyya Mai mulkin kasa APC ta ce ta kusa fara yakin neman zaben Tinubu/Shettima a matsayin yan takarar shugaban kasa da mataimaki.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Gwamna Simon Lalong ne ya bayayana hakan ga manema Labarai a Abuja.
Lalong wanda shi ne shugaban gangamin yakin neman zaben shugaban kasa ya bayyana hakan bayan kammala sa ido kan gyara ofishin gangamin yakin neman zabensu da ke Abuja.
Gwamnan ya kuma gana da wasu ma’aikatan kwamitin yakin neman zaben, a kokarin tabbatar da cewa komai ya tafi daidai.
Ya kuma samu ganawa Da ɗan takarar shugabancin kasa, Asiwaju Bola Tinubu, a hedikwatar.