Jam’iyyar APC ta tsige gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, a matsayin shugaban kwamitin daukaka kara na babban taronta na kasa wanda aka shirya yi a ranar 26 ga watan Maris din shekarar nan ta 2022.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa yanzu haka kwamitin daukaka kara na zaben zai kasance karkashin Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti.
Idan dai za a iya tunawa a baya ne kwamitin riko na APC karkashin Gwamna Mai Mala Buni ya nada Abiodun a matsayin shugaban kwamitin daukaka kara na zaben.
Sai dai a sabon jerin sunayen ‘yan kwamitin taron da mukaddashin shugaban jam’iyyar, Gwamna Abubakar Sanni Bello ya fitar a ranar Laraba, an maye gurbin sunan Abiodun da na Gwamna Fayemi.
A cikin jerin sunayen, Gwamna Abiodun ya zama shugaban kwamitin sufuri da tsare tsare.
Comments 1