Shugabancin jam’iyyar All Progressives Grand Alliance na kasa APGA ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan wakilan jam’iyyar a ranar Lahadi a Owerri, babban birnin jihar Imo.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin da ta gabata ta hannun sakataren yada labaranta na kasa, Tex Okechukwu, jam’iyyar ta ce an kai wa jami’anta hari a lokacin zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar,kamar yadda Punch ta rahoto.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hatsari Ne Fitowar Melaye A Matsayin Dan Takarar Gwamna __ Tsohon Mataimakin Gwamna
“Muna bakin ciki da yadda wasu marasa kishin kasa da ‘yan siyasa suka mayar da yanayin siyasarmu sannu a hankali.
“Muna so mu bayyana a fili cewa harin da wani wanda bai cancanta ba ko kuma aka ba shi izinin shiga zaben fidda gwanin da aka yi wa mambobinmu ba shi da tushe balle makama kuma ba za a amince da shi ba.
“Muna yin Allah wadai da wannan abin kunya na wanda ya shirya kai hare-haren, wanda ya yi amfani da ‘yan daba da jami’an tsaro masu fakewa da juna wajen raunata wakilai da jami’an jam’iyyar mu tare da goyon bayan wani jigon siyasa a jihar da ba a bayyana sunansa ba.
“Abin da ya faru a Owerri a ranar Lahadi babban aiki ne na rashin da’a, cin zarafi da wariyar launin fata da bai kamata wata al’umma ta halal ta amince da su ba,” in ji jam’iyyar.
A cewar sakataren yada labaran, wanda ya kai harin “ya zo ne domin sayan fom din takarar gwamnan jihar Imo. A lokacin da Kwamitin Waiver ya bibiyi takardunta daga baya, an gano cewa takardar neman ba bu sunan ta a ciki kuma har yanzu ba ta yi murabus daga APC ba. Bisa karfin wannan binciken, kwamitin ya ba da shawarar a ki amincewa da bukatar ta na neman a yi watsi da ita. Kwamitin Ayyuka na kasa ya yi haka ta hanyar amincewa da shawarar kwamitin Waiver.
“Abin takaici ne kuma abin kunya ne yadda ba tare da neman hakkin jam’iyyar ba, ta shirya ‘yan daba tare da kutsa kai wurin zaben fidda gwani a ranar Lahadi, inda ta lalata dukiyoyin jam’iyyar tare da bar wakilanta cikin mummunan rauni.
Jam’iyyar ta sha alwashin cewa za ta dauki “dukkan matakin da doka ta tanada domin neman adalci domin kaucewa faruwar wani abu a nan gaba.
A wani labarin kuma, Sabbin Takardun Kuɗin Naira Sun Yi Batan Dabo A Wasu Jihohi
Wata daya bayan dawo da tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1,000, wasu mazauna Anambra sun koka kan rashin samun sabbin takardun a bankuna da dama a jihar.
Wasu daga cikinsu sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Awka a ranar Litinin cewa da kyar suke kammala hada-hadar da sabbin takardun kudi na Naira saboda babu su.